Mun sha mamaki a Amurka —Hadiza Gabon

Hakkin mallakar hoto Hafizu Bello
Image caption Hadiza Gabon da Hauwa Maina da kuma sauran abokan tafiyarsu 'yan Kannywood, da kuma abokan karatunsu a Amurka

Hadiza ta bayyana tafiyarsu Amurka da cewa kwaliya ta biya kudin sabulu.

A hirar da BBC ta yi jarumar da kuma wasu daga cikin wadanda suka yi tafiyar, dukkannin su sun bayyana irin darasin da suka koyo a ziyarar da suka kai cibiyar shirya fina-finan ta duniya.

Sun kuma yi amanna da cewa abin da suka koya zai taimakawa shirin fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood a Najeriya.

A watan da ya gabata ne 'yan Kannywood din suka tafi Amurka halarta wani taron karo ilimi, sun dawo gida a makon jiya.

Ga hirar da Yakubu Liman ya yi da Hadiza Gabon da kuma Hauwa Maina.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti