Nijer da Chadi za su kafa rundunonin soji

Hakkin mallakar hoto AFP

Kasashen Yammacin Afrika da ke yankin Sahel za su kafa rundunoni na musamman domin yaki da ta'addanci.

Ministocin tsaro na kasashen Nijer da Chadi da Burkina Faso da Mali da kuma Mauritania sun ce za su yi aiki tare domin kafa kananan rundunonin tafi-da-gidanka, wadda kowacenta za ta kunshi kimanin goggagun dakaru dari.

A taron da suka yi a N'Djamena, babban birnin Chadi, ministocin sun ce za a tura dakarun zuwa duk wani wurin da 'yan ta'adda suka bula domin tunkarar su.

Tarayyar Turai ce za ta dauki nauyin rundunonin, wadanda za su dauki salon na kasar Sipaniya da aka yi amfani dasu wajen yakar 'yan aware na Basque.

Kasashen yankin Sahel dai na fuskantar matsalar kungiyoyi masu alaka da Al Qaeda wadanda kwanaki suka kai hare-hare a otel a Mali da kuma a Burkina Faso.

'Yan Boko Haram ma na Najeriya suna yawan kai hare-hare a kasashen da ke makwabtaka da ita a shiyyar arewa-maso-gabas.

Karin bayani