'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Istanbul.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar nuna goyon bayan 'yancin 'yan jarida

'Yan sanda a Turkiyya sun tarwatsa wata zanga-zangar nuna goyon baya ga yancin yan jarida a Istanbul.

Masu zanga-zangar sun hallara ne a kofar ofishin jarida mafi girma a kasar, Zaman, domin nuna adawa da kwace ofishin da gwamnati ta yi.

Anyi amfani da borkonon tsohuwa da bututan fesa ruwa akan masu zanga-zangar yayinda suke kuwwar cewa ba za'a murkushe 'yancin aikin jarida ba.

Rahotannin kafafen yada labaran kasar sunce an kori ma'aikatan kamfanin jaridar da dama.

Kasashen yamma da 'yan adawa a Turkiyyar sun yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin ta dauka.