An yake wa attajirin Iran hukunci kisa

Wata kotu a Iran ta yanke wa mutumin da ya fi kowa arziki a kasar hukuncin kisa, bayan ta same shi da laifin cin hanci da rashawa.

An tuhumi Babak Zanjani da yin almundahana ta kudi dala bilyan ukku.

Mista Zanjani, wanda 'biloniya' ne, ya yi aikin gano hanyoyin tauye takunkumin da kasahen Yamma suka saka wa Iran, wanda ya bata damar rika saida wani bangare na manta.

To amma kuma an zarge shi da yin amfani da wacce damar wajen arzita kansa.

An kama shi ne a shekara ta 2013 bayan da Shugaba Hassan Rouhani ya bada umurnin a yaki cin hanci da rashawa, musamman ma akan wadanda ya kira 'yan gata masu ci-da-gumin takunkumin da aka saka wa kasar.