NATO za ta yaki masu safarar mutane

Ma'aikatan ceto a tekun Aegean Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daruruwan mutane ke kasadar tsallaka tekun Aegean a cikin kwale-kwale a kowacce rana.

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce za ta fadada ayyukanta a tekun Aagean, a daidai lokacin da ake shirin fara wani taro da nufin duba hanyoyin hana masu gudun-hijira shiga Turai.

Kungiyar NATOn ta ce za ta girke jiragen yakinta a kan iyakokin Girka da Turkiyya da ke Teku, tare da yin aiki kafada da kafada da hukumar da ke kula da iyakokin tarayyar Turai.

A taron, wanda za a fara yau din nan a Brussels, shugabannin kungiyar Tarayyar turan za su matsa-lamba ga kasar Turkiyya domin ta hana wa mutane fita daga kasarta, kana ta karbi 'yan ci-ranin da za mika mata daga kasashen Tarayyar Turai.

Ita kuma Tarayyar Turan, a bangare guda za ta fitar da wani shiri na karbar wasu masu gudun-hijirar da suka shiga kasar Turkiyyar don sake tsugunar da su a Turai.