Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan Boko Haram da dama a wani farmaki da ta kai a kauyukan Dure na daya da Dure na biyu, da kuma Jango da Dibiye da ke jihar Borno.

Rundunar ta kuma ce dakarunta sun yi ba-ta-kashi da 'yan kungiyar, amma kuma daga bisani sojojin sun ci karfinsu.

A ranar Asabar ma rundunar ta ba da sanarwar cewa tare da hadin gwiwar jami'ai na musamman sun yi amfani da wasu bayanai na sirri, inda suka afka wa 'yan kungiyar a garin Doksa da ke karamar hukumar Biu na jihar Bornon.

Rikicin Boko Haram da ya addabi arewa maso gabashin Najeriya da kassahe makofta irin su Kamaru, da Nijar da kuma Chadi, ya raba mutane da muhallansu.