Hatsarin mota ya hallaka mutane 18

Image caption Hatsarin mota ya zama ruwan dare a Najeriya

Mutane 18 sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru a kan titin Bauchi zuwa Jos.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi, yayin da wata babbar mota da motar bas suka yi karo a wani kauye Buzaye, da ke karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi..

Rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi ta ce mutane 17 daga cikin 18 din sun kone kurmus ta yadda har ba za a iya gane su ba, yayin da motar bas din da suke ciki ta kama da wuta.

Rahotanni sun ce babbar motar na kan hanyar zuwa Jos ne amma motar bas din ta fito ne daga Abuja zuwa Bauchi.

Hadarin mota ya zama ruwan dare a Najeriya, sakamakon rashin kyawun tituna da tukin ganganci da kuma rashin kula da ababen hawar.