Kotu ta ki bayar da belin Badeh

Image caption EFCC na zargin Alex Badeh ta sace dala miliyan 20

Babbar kotun tarayyar Nigeria ta ki bayar da belin tsohon babban hafsan sojin kasar Air chief Marshal Alex Badeh me ritaya.

Babbar kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta gurfanar da Mista Badeh, a gabanta ranar Litini.

Hukumar ta zargi Mista Badeh da laifin satar kudi mallakin Rundunar sojin sama ta Najeriyar kimanin dala miliyan 20, a lokacin da ya ke babban hafsan sojin kasar, domin sayen filaye.

Rahotanni sun ce Mista Badeh ya gina katafaren gida na kasaita har ma da rukunin shaguna.

Mista Badeh dai ya musanta wannan zargi.

Raliya Zubairu ta yi wa Ahmad Abba Abdullahi karin bayani kan yadda zaman kotun ya kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Air Marshal Badeh mai ritaya shi ne tsohon babban hafsan sojin Najeriya karkashin mulkin shugaba Goodluck Jonathan. Yana daga cikin wasu manyan jiga-jigan tsoffin sojojin kasar da EFCC ke gudanar da bincike a kansu, bisa zarginsu da almundahana.