'Isra'ela ta yi karya' - Amurka

Barack Obama Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Amurka ta ce ta sha mamaki dan Mr Netanyahu bai sanar da ya fasa halartar taron ba a hukumance.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce Firayim Ministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya soke wani taron da ake sa ran zai yi da shugaba Barak Obama a cikin wannan watan.

Kakakin shugaba Obama ya ce mamaki ya kama gwamnatin Amurka, saboda Mista Benjamen Netanyahun bai sanar da ita ba sai ta kafafen yada labarai kawai ta ji Firayim Ministan Isra'ilar ya fasa halartar taron.

Kakakin fadar White House din ya ce hanzarin da Isra'ila ke gabatarwa cewa an fasa yin taron saboda Amurka ba ta shiga da batun ganawa da Firayim Ministan Isra'ilar ba karya ce tsagwaronta.