Kwamfutar Mac ta gamu da masu kutse

An yi wa kwamfutar mac kutse

Asalin hoton, palo Alto

Bayanan hoto,

An yi wa kwamfutar mac kutse

A karon farko masu kutse da kan rufe manhajojin masu amfani da kwamfuta da nufin karbar kudi kafin su bude sun yi nasarar shiga kwamfutar Mac ta kamfanin Apple.

Masu bincike sun ce wannan ne karon farko da aka yi wa kwamfutar Mac irin wannan kutsen.

Ana dai boye manhajar KeRangers da ke yin kutsen da ita ne a cikin wani samfurin manhajar BitTorrent da ake kira "Transmission."

Masu kamfanin Transmission da Apple duka sun ce suna daukar matakai wajen hana yaduwar manhajar masu kutsen.

Ita dai manhajar Tramsmission na ba da damar sauke manhajar BitTorrent tare da turawa ga abokan hulda abubuwan da suka shafi wakoki da fina-finai.

Matakin da Apple ya fara dauka bayana sanar da shi wannan matsala shi ne soke shaidar kamfanin da ke yin manhaja mai ba da damar yada wadda ake yin kutsen da ita don kare masu amfani da kwamfutarsa.