An kashe 'yan Al Shabab 150

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin Amurka marar matuki ya hallaka 'yan Al Shabab

Rundunar sojin Amurka ta ce ta kashe fiye da mayakan Al Shabab 150 a wani harin jirgi marar matuki.

Fadar gwamnatin Amurka ta ce an kai harin jirgi marar matukin ne a ranar Asabar.

Ta kuma ce an yi niyyar kai harin ne kan wani sansanin bayar da horo a arewacin Mogadishu, babban birnin kasar.

Amurka ta ce mayakan na shirye-shiryen kai wani babban hari ne.

Har yanzu dai kungiyar AL Shabab bata mayar da martani kan lamarin ba.

Karin bayani