Kalaman Trump na kama da na Hitler

Shugaba Enrique Pena Nieto Hakkin mallakar hoto AP
Image caption kalaman Mr Trump kan hana musualmai shiga Amurka ya janyo cece-kuce a kwanakin baya.

Shugaban kasar Mexico Enrique Peña Nieto shaida wa wata jaridar kasar cewa irin kalaman da Donald Trump ke yi, mai neman takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar suna kama da kalaman Adolf Hitler da Benito Mussolini.

Mr Trump dai ya yi wani furuci mai tunasarwa a kan 'yan ci-ranin da suka fito daga Mexico a yakin neman zabensa, inda ya ambaci wasu da cewa masu fyade ne, har ma ya yi alkawarin tilasta wa Mexico daukar dawainiyar gina ganuwa tsakaninta da Amurka.

Kazalika, a wata hira da wata jaridar, Shugaba Enrique Peña Nieto ya ce Mr Trump yana bata dangantakar da ke tsakanin Mexico da Amurka.