'Yan cirani za su samu sassauci a Turkiyya

Shugabannin kasashen Turai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a ci gaba da tattaunawa a ranar 17 ga wannan watan.

Shugaban Majalisar kungiyar Tarayyar Turai, Donald Tusk ya ce lokacin shiga Turai ba bisa ka'ida ba ya wuce.

Ya yi wannan furuci ne, sakamakon yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da shugabannin kasar Turkiyya, duk kuwa da cewa sai a nan gaba ne za tattauna a kan cikakkiyar yarjejeniyar yaki da bakin hauren a wanin taron da za a yi a mako mai zuwa.

Mista Tusk ya shaida wa wani taron manema labarai cewa za a taka-birki ga masu gudun-hijirar da ke ratsawa ta tekun Turkiyya, haka kuma wadanda suka riga suka isa Girka za a mai da su Turkiyya.

Kungiyar Tarayyar Turai a nata bangaren za ta samar da sama da dala biliyon uku don aikin agaji, da kuma karin wani kudi don kula da masu gudun-hijirar da ke Turkiyya, wadanda suka fito daga Syria, kudin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce Turkiyyar na bukatarsa cikin gaggawa.

Firayim Ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu ya ce yana da kyau a kalli yarjejeniyar a matsayin wadda za ta share hanya ga kasarsa wajen shiga kungiyar Tarayyar Turai.