Rashin rufe layukan MTN ya taimaka wa BH

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta hallaka mutane da dama cikin shekaru shida

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan rashin rufe layukan wayar da ba a yi wa rijista ba na MTN ya taimakawa kungiyar Boko Haram.

Yana magana ne a karo na farko a bainar jama'a tun bayan da aka sanyawa kamfanin biyan tarar dala biliyan 5.2 sakamakon rashin karasa rijistar katunan wayar abokan cinikinsu.

Shugaban ya yi wannan magana ne lokacin da yake ganawa da takwaransa na Afrika ta Kudu Jacob Zuma, a Abuja.

Ya kara da cewa mayakan kungiyar Boko Haram suna amfani da katunan wayar da ba a yi musu rijista ba wajen gudanar da al'amuransu na kai hare-hare.

Ya ce "kun san 'yan ta'addana amfani da layukan da ba a yiwa rijista ba, kuma a tsakanin shekarar 2009 zuwa yau a kalla kungiyar Boko Haram ta kashe mutane a kalla 10,000."

Shugaba Buhari ya ce, damuwar gwamnatin tarayya ta fi yawa a kan tsaron kasa fiye da tarar da ake bin MTN.