Wani bene ya rufta a Legas

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana yawan samun afkuwar rugujewar gine-gine a birnin Legas da ke sanadiyyar rasa rayuka.

Jami'an kai agajin gaggawa NEMA, a jihar Legas a Nigeria na ci gaba da ceto mutanen da ake kyautata zato wani bene mai hawa biyar ya rufta da su.

An dai rawaito cewa an samu salwantar rayuka bayan ruftawar benen.

Kakakin hukumar ta NEMA a jihar, Ibrahim Farinloye, ya bayar da tabbacin cewa mutane hudu ne suka rasa rayukansu, amma kuma an ceto rayukan mutane biyar.

Ba a daukan lokaci mai tsawo ba tare da an samu afkuwar irin wannan lamarin ba a jihar Legas, kuma a shekarar da ta gabata ma wani babban coci ya rushe a birnin, inda yawancin wadanda abin ya rutsa dasu 'yan kasar Afrika Ta kudu ne.