Yau take ranar mata ta duniya

Wani sabon bincike na duniya ya nuna cewar mata sun samu ci gaba kadan a wuraren aikinsu cikin shekaru 20 da su ka gabata.

Rahoton wanda kungiyar kwadago ta duniya ta wallafa, domin murnar bikin ranar mata ta duniya -- ya ce mata suna cigaba da fuskantar kalubale wajen samun ayyukan yi masu kyau.

Kasar Rasha ce kan gaba a jerin kasashen da akasarin mata ke jagorantar manyan mukamai na kasuwanci a kasar, sai kasar Phillippines da kuma Lithuania.

A Japan, mata ne ke rike da kashi bakwai cikin 100 na manyan mukamai a wuraren aiki, dalilin da yasa kasar ta zamo daga cikin kasashen da ke karshe a jerin sunayen kasashen da mata suka samu ci gaba.