Shin ko matan Saudiyya na fuskantar matsin lamba mai tsanani?

Image caption Ko mata suna fuskantar matsain lamba a Saudiyya

Shin ko matan Saudiyya na fuskantar matsin lamba mai tsanani?

Shin za ka so zama a Saudiyya a matsayin mace? Duk da irin laarn da ake samu dangane da su, wanda ba lallai haka abin yake ba?

Ana ganin kamar rayuwar mata na karkashin mulkin danniya a Saudiyya, ganin cewa an haramta musu wasu abubuwa kamar tukin mota kuma an tursasa musu kasancewa karkashin kulawar wakili namiji wanda ake ganin hakan ya hana su samun cikakken 'yanci.

BBC ta yi labarai da dama da suka bazu kamar wutar daji wadanda ke nuna yadda wannan takura ke shafar rayuwar mata.

Image caption Matan Saudiyya da dama sun musanta batun cewa suna fuskantar matsain lamba

Amma da yawa daga cikin labaran nan sun nuna yadda mata ke amfani da kafofin sada zumunta na zamani don a ji kukansu, suna masu kalubalantar yadda al'ummarsu ke kallonsu da kuma yadda duniya take musu kudin goro.

Daga cikin shirin da BBC ta kaddamar na "'Yan Saudiyya a kafafen sada zumunta," mun tambayi matan kasar: "Shin suna fuskantar irin wannan kuntatawa da ake babatu a kai?"

Idan aka zo batun matan Saudiyya, a iya cewa akwai irin yadda mafi yawan mutanen duniya ke kallon lamarinsu.

Rashin daidaito da kuma har da ma rashin 'yancin tuka mota.

Amma, mata da dama a Saudiyya sun ce wannan wani kudin goro ne kawai da ake musu, ba haka ainihin maganar take ba.

Samar Al Morgan 'yar jarida ce a Saudiyya, ta ce, "Matan Saudiyya sun sha bambam matuka da sauran mata, ina daga cikin matan da basu yadda da irin kallon da kaffofin yada labaran kasashen yamma suke mana ba."

Don haka BBC ta tambayi matan Saudiyya da dama kan ko da gaske ne matan kasar na fuskantar matukar matsin lamba kamar yadda ake ta kwakwazo?

NOURAH AL-SHABAAN kuwa babbar darakta ce ta wani kamfani: "A matsayina na mace 'yar Saudiyya ban taba fuskantar wata takura ta kowanne bangare ba, a majalisar dokokinmu muna da mata fiye da 30."

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption Mata sun samu 'yancin shiga al'amuran siyasa

Tana magana ne a kan al'amarin da ya faru na baya-bayan wadda ake son a bai wa mata damar kada kuri'a da kuma shiga cikin al'amuran majalisar dokoki.

To ko suna da hujja?

Mafi yawan mata a Saudiyya sun kammala karatun jami'a fiye da maza. Kuma wani abu da ya sha bambam da abin da aka saba ji shi ne matan Saudiyya suna iya yin aiki, kuma a takaice ma sun samu ci gaba a fannoni daban-daban.

Akwai mata amsu shirya fina-finai

Ana samun Lauya mace 'yar Saudiyya

Sannan an samu mace ta farko a kasar wacce take daf da zama daktar ilimi a kan fasahar binciken halittu

Kuma idan aka zo batun kafofin sada zumunta na zamani ma, bari kawai a ce anan ma ba a barsu a baya ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Saudiyya da kafafen sada zumunta na zamani

Ga maudu'ai da suka samar a shafukan sada zumuntar kamar haka: #26th of October driving #WomanAttacksHarasserInDamam #ParliamentWithoutSeats #GirlConfrontsReligiousPolice

Mata za su iya yin abubuwa da dama a Saudiyya kuma suna yi din, amma abin da wasu ke ganin yana dankwafar da su shi ne suna bukatar wakili namiji a kowanne al'amari da za su yi.

NOURAH AL HARBI wata daliba ce, ta kuma, "Wasu daga cikin abubuwan da muke fatan samun sauyi a tattare da su sun hada da, yi wa wasu dokoki gyaran fuska kamar samun damar mallakar katin shaidar zama dan kasa ba tare da bukatar wakili ba."

Hamsah Al-Sinousy wata mai bincike ce da ta ce, "Wasu daga cikin matsalolin da mata ke fuskanta sun hada da na zama a gidan yari. Ba a iya sakin mata daga gidan yari ba tare da izinin wakilinsu ba, wanda hakan babbar matsala ce saboda wasu ba sa barinsu su dawo. Akwai kuma matsalar cin zarafin mata da maza ke yi, wasu daga cikin irin wadannan da wannan abu ya rutsa da su ba su da wani abin yi sai dai su yi gum da bakinsu."

Wani labarin kuma shi ne na Shahd.

Hakkin mallakar hoto General Electric
Image caption Matan Saudiyya a wuraren ayyukansu

Ta ce, "Sunana Shahd, shekarata 20 kuma na taso ne karkashin uba mai cin zarafina. Shekaru biyar da suka gabata mahaifiyata ta je kotu don neman saki. Uwata ta yi ta fafutuka don ganin mun girma a wajenta, amma saboda dokar samun wakili sai mahaifinmu ya yi nasara a kanta ta hanyar barinmu mu girma a hannunsa.. Abin da kawai mahaifiyata ta bukata shi ne saki, amma ba a yi mata adalcin barinmu a hannunta ba."

A bayyane yake cewa in har ana maganar samun 'yanci to har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Kazalika, mata da dama a Saudiyya sun ce kasancewar su wadanda danniya ta taba shafa yana sa fafutukarsu ta neman 'yanci na kara zafi.

Samar kuwa sai ta ce, "Bana goyon bayan suka, amma ta wani bangare ina yarda da wasu soke-soken, sai dai ina so kafofin yada labaran kasashen yamma su dinga adalci su kuma dinga fadan irin dadi da ci gaban da matan Saudiyya ke samu."

Karin bayani