Trump da Clinton sun ƙara yin zarra

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Donald Trump shi ne a gaba-gaba cikin 'yan takarar republican, a zaben fidda gwani da ke gudana a jihohin Amurka.

Dan takarar Amurka na jam'iyyar republicans, Donald Trump, ya sa kwazo wajen ganin shi ne zababben da zai jagoranci jam'iyyarsa a takarar shugaban kasar, bayan zabben fidda gwanin da aka gudanar a kwan-kwanan nan.

Hamshakin dan kasuwar, wanda ba asalin dan siyasa bane, ya lashe zaben fidda gwani a jihohin Michigan da Mississippi da Hawaii, duk da sukar da ya sha daga manyan 'yan jam'iyyar tasa cikin makon da ya gabata.

Babban abokin hamayyarsa a jam'iyyar Ted Cruz, ya lashe 'yar karamar jihar Idaho.

A wani bangaren kuma, yakin neman zaben a jam'iyya mai mulki ta Democrats, Bernie Sanders ya bada mamaki bayan ya yi nasarar a kan abokiyar takarasa Hillary Clinton, bayan ya lashe zaben jihar Michigan.

Sanders ya ce ya yi matukar farin ciki a daren ranar a Michigan.

Duk da haka dai Misis Clinton ta yi babban nasara a zaben da aka gudanar ranar Talata, a Mississippi, inda yta kara mata tazarar tsakaninta da Sanders.

Wakilin BBC ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa kudurin Sanders game da tattalin arziki rage na cigaba da farin jini wajen al'umma.