An dade ana son rarraba NNPC - Tuggar

An raba Kamfanin mai na Nigeria NNPC, zuwa kamfanoni bakwai inda ko wane bangare ke da shugaba.

A ranar Talata ne minstan mai na kasa, Emmanuel Ibe Kachikwu, ya fitar da wannan sanarwar a Abuja biyo bayan amincewar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi da hakan.

Tuni masu lura da al'amuran da suka shafi harkokin mai da iskar gas, suka soma tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan matakin.

Honorabul Yusuf Tuggar, na daya daga cikin masu lura da al'amura da kuma bayar da shawara ga wannan bangare, ga kuma bayanin da ya yi wa Ibrahim Mijinyawa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A shekarar 2013 ne dai tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Mallam Sanusi Lamido Sanusi ya ce NNPC din ya kasa bayyana yadda ya kashe wasu kudade da yawansu ya kai biliyoyin daloli.