Kano: An fito da sabon tsarin Hajjin bana

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar Alhazai a jihar Kano ta ce daga yanzu ba za ta sake barin tsofaffi da marasa lafiya su tafi aikin hajji ba, matukar ba su da dan rakiyar da zai kula da su a kasar Saudiya.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne a wajen wani taron masu-ruwa-da-tsaki da ta gudanar domin neman mafita daga matsalolin da aka fuskanta yayin aikin hajjin bara.

Daga yanzu hukumar ta ce za ta dauki ragamar tantance maniyyata, maimakon tura su asibitoci, wadanda ake zargin cewa suna cuwa-cuwa.

Malam Abba Yakubu shi ne babban sakataren hukumar, ya ce dalilin daukar wannan mataki ya biyo bayan irin wahalar da tsofaffi da marasa lafiya ke sha ne a lokacin aikin hajjin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dan haka suka yanke wannan hukunci, Malam Yakubu ya ce za su dauki dukkan matakan da suka kamata dan tabbatar da an yi amfani da dokar.