Ma'aikatan NNPC sun shiga yajin aiki

Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyoyin ma'aikatan mai na NNPC a Nigeria, ta shiga yajin aiki bisa rarraba kamfanin na NNPC.

Kungiyoyin sun kuma rufe duka ofisoshin NNPC da ke fadin kasar.

Kungiyar ta ce shugaban NNPC din, Emmanuel Ibe Kacikwu bai shawarci masu ruwa da tsaki a kan batun ba, inda suka yi zargin cewa Mista Ibe, bai bi ka'ida.

A ranar Talata ne dai shugaban NNPC din ya sanar da raba kamfanin zuwa kafanoni bakwai bayan samun amincewar shugabn kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai a yanzu babu tabbas ko yajin aiki zai shafi ayyukan hako danyen mai a yankin Naija Delta.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Akwai fargabar cewa wannan yajin aikin zai iya jawo karancin man fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.