Bankin duniya zai tallafa wa arewacin Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin bayar da agaji na duniya na fadan muhimmancin ilimin yara mata

Bankin duniya ya ware dala miliyan 100 don bunkasa ilimin yara mata a jihohi biyar da ke arewacin Najeriya.

Jihohin sun hada da Kano da Kaduna da Sokoto da Katsina da kuma Jigawa.

Wata babbar jami'ar bankin, Tunde Adekola, wadda ta kaddsamar da shirin a Katsina, ta ce za a yi amfani da kudin ne wajen bai wa Malamai horo.

Misis Adekola ta kara da cewa kudin za kuma su taimaka wajen gyaran makarantu da daukar nauyin karatun yara da kuma samar da kayan amfanin karatu.