''tuntuni akwai batun rarraba NNPC''- Tuggar

Emmanuel Ibe Kachikwu: Ministan Mai na Nigeria

Asalin hoton, NNPC

Bayanan hoto,

Emmanuel Ibe Kachikwu: Ministan Mai na Nigeria

An raba Kamfanin mai na Nigeria NNPC, ya rarrabu zuwa kamfanoni bakwai inda ko wane bangare ke da shugaba.

A ranar Talata ne minstan mai na kasa, Emmanuel Ibe Kachikwu, ya fitar da wannan sanarwar a Abuja biyo bayan amincewar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi da hakan.

Bello Rabiu shi ne zai shuigabanci kamfanin Upstream, wanda ke kula da rijiyoyin mai na kasa da kuma binciko in da akwai yiwuwar za a iya samun danyen mai, Henry Ikem-Oniy shi ma zai shugabanci Downstream, kamfanin da ke kula da rijiyoyin mai na cikin teku, sai Saudu Mohammed wanda zai jagoranci kamfanin kula da Isakar gas da Lantarki, Anibor Kragha, shine shugaban kamfanin kula da matatun mai na kasa, sai Babatunde Adeniran da zai shugabanci kamfanin kasuwanci, sai Isiaka Abdulrazaq da zai shugabanci kamfanin tsare-tsaren ayyuka da kudade na kamfanonin.

Mista kachikwu ya ce sabbin kamfanonin zasu mayar da hankali ne kawai kan kasuwanci kamar yadda sauran kamfanonin mai na duniya suke yi.

A shekarar 2013 ne dai tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Mallam Sanusi Lamido Sanusi ya ce NNPC din ya kasa bayyana yadda ya kashe wasu kudade da yawansu ya kai biliyoyin daloli.