An dakile yunkurin sata a bankin Bangladesh

Hakkin mallakar hoto Focus Bangla
Image caption Masu kutsen sun sace dala miliyan tamanin wanda shi ne satar banki mafi girma da aka taba yi a kasar.

Wasu masu kutse a Internet sun yi kokarin satar kimanin dala biliyan daya a babban bankin kasar Bangladesh.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya ambato wa su jami'an bankin na cewa gungun masu kutsen sun yi amfani da wasu takardu da aka sace inda suka gabatar da bukatar neman iznin tura kudaden a wasu asusun ajiya.

Jami'an suka ce idan da ba'a binciki neman iznin tura kudaden da suka gabatar ba, da masu kutsen sun yi nasarar sace kimanin dala biliyan daya.

An gano yunkurin ne bayan da aka ga kudaden da ake neman turawa sun yi yawa sosai lamarin da ya sa aka fara shakku kan sahihanci neman iznin tura kudaden.

Sai dai an yi amannar cewa masu kutsen sun yi nasarar sace kimanin dala miliyan tamanin, wanda shi ne satar banki mafi girma da aka taba yi a kasar.

Kudaden da aka sace an tura su ne zuwa wasu asusun ajiya a kasashen Sri Lanka da Philippines kuma jami'an babban bankin na ci gaba da kokarin kwato kudaden.