China da Korea ta Arewa na takun saka

Kasar China ta ce za ta haramta wa jiragen ruwan Koriya ta arewa shiga kasarta.

A wani taron da jiga-jigan jam'iyyar Communinist Party mai mulkin kasar suka yi a Beijing, Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya ce za a haramta wa baki dayan jiragen ruwan Koriya ta arewa shiga Sin.

Kafafen yada labaran Sin din sun ambato Ma'aikatar harkokin wajen tana cewa China na aiwatar da kudirin da majalisar dinkin duniya ta zartar ne a kan Koriya ta arewa saboda gwajin nukiliyar da ta yi.

Ita ma Japan ta ce sam ba ta amince da matakin da Koriya ta arewar ta dauka na harba wasu makamai masu linzami biyu, yau din nan ba.

Makaman sun yi tafiyar kusan kilomita 500, kana suka fada cikin ruwan da ke birnin Wonsan.

Hakkin mallakar hoto XINHUA
Image caption China ta bi sauran kasashen duniya na daukar mataki kan Korea ta Arewa

A watan Janairun da ya wuce ma, Koriya ta arewar ta yi biris da barazanar kakaba mata takunkumin da aka ce za a yi, ta yi gwajin wasu makaman nukiliya.