Kotu ta bayar da belin Alex Badeh

Image caption Ana zargin Badeh da aikata zamba cikin amince

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bayar da belin tsohon hafsan hafsoshin sojin Nigeria, Air chief Marshal Alex Badeh karkashin wasu tsauraran sharudda.

Sharuddan kamar yadda alkalin kotun Mai sharia Okon Ebang ya karanto, su sun hada biyan kudi Naira biliyan biyu da kuma kawo mutane biyu da za su tsaya masa wadanda kowanne zai bayar da Naira biliyan daya jingina.

Kuma dole ne mutanen su kasance sun mallaki wata kadara a birnin Abuja.

A ranar litinin ne hukumar EFCC ta gurfanar da Mista Badeh gaban wannan kotun bisa zarginsa da tafka laifuka 10 masu alaka da zamba cikin aminci da almundahanar biliyoyin naira.

Rahotanni sun ce Mista Badeh ya gina katafaren gida na kasaita har ma da rukunin shaguna a Abuja.

Mista Badeh dai ya musanta wadannan zarge-zargen.