Fulani sun koka a kan sare dazuzzuka

Image caption Fulanin sun ce sare itatuwa a Gandun Dajin na barazana ga rayuwar dabbobin su

A Nigeria, wa su Fulani makiyaya a Jihar Kaduna sun nuna damuwa bisa sare saren bishiyoyi da dazuzzuka a Gandun Daji na Kachia wato Kachia Grazing Reserve da ke Kudancin jahar.

Fulanin wadanda suka dogara kacokan kan kiwo na cewa wannan dabi'a ta sare saren itatuwa a Gandun Dajin na barazana ga rayuwar su baki daya.

Karancin wuraren kiwo na cikin manyan matsalolin da ke haddasa rikici tsakanin manoma da makiyaya a wurare da dama a Najeriya.

Daya daga cikin shugabannin Fulanin Ardo Toro Bello Lodduga ya shaida wa BBC cewa suna bukatar gwamnatin jihar ta dauki mataki cikin gaggawa don kawo karshen sare itatuwa a Gandun Dajin.