APC za ta ladaftar da Kwankwaso

Image caption Magoya bayan Kwankwaso sun nuna rashin da'a a wajen ta'aziyya

Jam'iyyar APC a jihar Kano ta yi Allah wadai da halin rashin da'a da ta ce magoya bayan tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka nuna a lokacin da sanatan ya kai ziyarar ta'aziyya bisa rasuwar mahaifiyar gwamnan jihar mai ci Dr. Abdulllahi Umar Ganduje.

Jam'iyyar tace ba ta ji dadin yadda aka mayar da ta'aziyyar tamkar wani gangamin siyasa ba, inda aka gayyato mutane da dama, sannan wasu suna rera taken tsohon gwamna Kwankwaso.

A wajen wani taron manema labarai da jam'iyyar ta yi tace abin takaici ne yadda magoya bayan tsohon gwamnan, kuma sanata a yanzu suka je wajen gaisuwar dauke da muggan makamai, wasu kuma suna rarraba takardun yakin neman zaben Kwankwaso, gami kuma da furta kalamai na batanci.

Shugaban jam'iyyar ta APC a Kano wanda ya yiwa manema labarai bayani yace jam'iyyar ta yi takaicin abinda ya faru, kuma ba su da hannu a faruwar sa, sannan za ta rubutawa uwar jam'iyyar ta kasa abinda ya faru a hukumance.

Ana dai ganin wannan mataki zai kara futo da rashin jituwa tsakanin magoya bayan tsohon gwamnan da kuma na wanda ya gaje shi, wato gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje