Ma'aikatan NNPC sun janye yajin aiki

Hakkin mallakar hoto NNPC Website

A Nigeria kungiyoyin kwadago na ma'aikatan NNPC sun janye yajin aikin da suka shiga a ranar Alhamis.

Hakan dai ya biyo bayan wata ganawa da suka yi da minista a ma'aikatar man fetur, Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu a Abuja.

Daya daga cikin 'yan kwadagon da suka halarci tattaunawar, Saleh Abdullahi ya shaida wa BBC cewa kungiyoyin sun amince a ci gaba da garambawul din da aka sanar za a yi wa katafaren kamfain na kasa.

Haka kuma ministan ya kafa wani kwamiti wanda zai tabbatar daga yanzu za a dinga shawara da kungiyoyin kwadagon yayin da ake aiwatar da gyaran fuskar.

Ministan kuma ya basu tabbacin cewa babu wanda zai rasa aikinsa a dalilin sabbin sauye-sauyen da gyaran fuskar zai kawo.

A ranar Talata ne dai mista Kachikwu ya sanar da rarraba kamfanin na NNPC zuwa sabbin sassa bakwai, bayan ya samu amincewar shugabn Najeriya Muhammadu Bu