Mafarauta na kashe Karkanda a Afirka

Karkanda Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu cire hauren Karkandar na kai wa yankin Asia ne dan saidawa kan makudan kudade.

Wata kididdiga ta nuna cewa yanzu shekara ta shida kenan a jere ana samun karuwar adadin Karkanda da mafarauta ke kashewa a nahiyar Afirka.

Cibiyar da ke fafutukar kare hakkin halittu ce ta fitar da alkaluman, wadanda suka nuna cewa a bara kadai an kashe sama da Karkanda 1300 da nufin cire musu haurukansu.

Ana danganta karuwar farautar Karkandan ne ga bukatar haurensu a gabashin Asiya, inda wasu suka yi imani da cewa haure na maganin wasu cututtuka.

Wakilin BBC ya ce idan aka ci gaba da farautar Karkandan zuwa shekaru goma masu zuwa, to, adadin wadanda za su rage ba zai taka kara ya karya ba.