Ana karancin Biredi a jihar Rivers

Mazauna Jihar Rivers ta kudu maso kudancin Najeriya sun shiga wani hali sakamakon matsanancin karancin biredi da ake fama da shi a jihar.

An fuskanci Karancin biredin ne sakamakon wani yajin aiki da masu gasa biredi suka shiga domin neman gwamnati ta dauki matakan da za su saukaka farashin kayayyakin da masu gasa biredin suke amfani da su.

Alhaji Adamu Kwanar Auyo wani mazaunin Fatakwal ne, babban birnin jihar ta Rivers, Yusuf Tijjani ya tambaye shi ta waya ko tun yaushe suke fama da wannan matsala?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti