Wata mata ta sace jaririya a Afrika ta Kudu

Wata kotu a Afrika ta Kudu ta samu wata mata da laifin sace jarirai daga wani asibiti shekara 20 da suka gabata.

A birnin Cape Town ne dai alkalin ya yanke cewa bayanin da matar ta fada na yadda a ka bata jaririyar, a matsayin tatsuniya.

A shekarar da ta gabata ne yarinyar ta hadu da iyalinta, bayan ta kulla kawance da wata yarinya a makaranta wacce su ke kama da ita sosai amma bata kai ta a shekaru ba.

Gwajin kwayoyin halitta da aka yi ne ya tabbatar da yaran biyu 'yan uwan juna ne.

Mahaifiyar 'yan matan ta fashe da kuka a lokacin da aka sanar cewa an kama matar da laifin sace 'yarta.