Kudirin Amurka ya fuskanci cikas

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kasashen uku sun ce kamata ya yi wanda aka samu da laifi ne zai fuskanci tuhuma.

Kasashen Rasha da Masar da kuma Senegal sun ki amince wa da shawarar tura daukacin dakarun sojojin wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya zuwa gida matukar suka yi ta fuskantar zargin cin zarafi da kuma lalata daga sauran mambobin su.

Kasashen uku sun ce yin hakan tamkar yin hukunci ne kuma kamata ya yi wanda aka samu da laifi ne zai fuskanci tuhuma.

Amurka ce dai ta gabatar da daftarin inda ta yi kira da a gaggauta daukar matakai na kawo karshen cin zarafi da kuma lalata musamman ga kananan yara a tsakanin dakarun wanzar da zaman lafiya.

Kudirin dai ya samu goyon bayan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon.