'Yan biyu masu uba daban-daban

Image caption 'Yan biyu masu uba daban-daban

Wata kungiyar gwajin kwayoyin halitta a Vietnam ta tabbatar da wani bincike da ya gano wasu 'yan biyu masu uba daban-daban.

An yi wa yaran gwajin kwayoyin halitta ne bayan da iyaye da 'yan uwa suka lura cewar ba sa kama da juna kwata-kwata.

Masana kimiyya na kiran wannan abu da "heteropaternal superfecundation," wato maniyyin mazaje biyu ne suke kyankyashe kwayaye daban-daban a lokaci guda.

Masana kimiyya dai sun ce wannan lamari abu ne da bai cika faruwa ba kuma mutane kalilan ne suka san irin hakan na faruwa a cikin al'umma.

Shugaban kungiyar gwajin kwayoyin halitta ta Vietnam, Farfesa Le Dinh Luong, ya ce sakamakon gwajin ya nuna 100 bisa 100 cewa tabbas yaran kowa da ubansa.

Sai dai ya ki bayyana iyalan yaran ko wajen zamasu saboda ya ce sun bukaci a boye hakan.