Me 'yan Amurka za su yi idan Trump ya yi nasara

Hakkin mallakar hoto Reuters

Donald Trump ya ci gaba da samun nasara a yakin da yake na neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, inda ya kara samunnasarori uku a zaben fidda gwani.

Kuma a duk inda Trump ya yi nasara, to sai kafofin sada zumunta su yi caa wajen bayyana ra'ayoyinsu.

A wannan karon an fiddo da maudu'i mai taken #ifTrumpwins, wanda ke nufin "idan Trump ya yi nasara," ya yi farin jini sosai a dandalin muhawara na Twitter, inda ya jawo muhawara mai zafi a fannin yakin neman zaben siyasar duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Haka kuma a lokacin da aka gabatar ban dariya na tsakar dae wato Comedy Central Midnight da karfe 12 dare, saka masu bin shirin a dandalin sada zumunta da Muhawara kusan 500,000 ne suka yi muhawara a kan maudu'in.

Sakonni biyu a twitter da @PoliticsJim ya sanya sun taimaka wajen fadada muhawarar da ake yi, inda sakon ya zagaya sau 6,000 a twitter. Dukanninsu sun yi ta barkwanci a kan sakon Trump na yakin neman zabe da ke cewa, "A kara daukaka Amurka kamar baya," wato "Make America Great Again".

Daya ya shafi barkwanci a kan ficaccen dan Amurka mai zane da kuma ma'aikacin gidan talabijin Bob Ross, wanda shirinsa na PBS na The Joy of Painting, wanda ke nufin jin dadin da ke tattare da yin zane, ya sa aka san shi sosai a duniya a shekarun 1980 da 1990.

Hakkin mallakar hoto

A wani ra'ayi da Jim ya bayar ya raina taken inda ya sauya da Cake, yayin da ya sauya taken yakin neman zaben na Trump zuwa " Bake America Cake Again," wanda ke nufin sake gasa Amurka tamkar fanke, taken da duk wani dan Amurka mai son kamfanin yin kayan abinci na fulawa kamar su mit fai da kek na Patisserie zai goyi baya, duk da banbancin siyasa.

Idan aka yi la'akari da giya da ruwa da nama da Trump ya je da shi wurin taron maneman labarai bayan ya yi nasara, hakan na nuna cewar babu wanda zai kwana da yunwa idan ya ci zabe.

A yayin da mu ke kan batun yunwa...jinjina ga Doomsdavid na samar da batun da ake tattaunawa kan mau'duin #ifTrumpwins da kuma Hunger Games formula.

Wannan ne samfuri na baya-bayan nan a kan rawar da kafafen yada labarai ke takawa a kan takarar shugabanci Amurka, bayan da aka yi zaben fidda gwani na jihohi 11 a ranar Super Tuesday.