Wani abu ya fashe a reshen CBN na Calabar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An tura jami'an tsaron zuwa ginin

Rahotannin daga Calabar, babban birnin jihar Cross River a Nijeriya, na cewa mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar wani abu a ginin babban bankin kasa CBN, reshen jihar.

Hukumomin 'yan sanda dai sun tabbatar hadarin inda suka ce mutane 21 ne suka samu raunuka.

Mataimakin sufeto janar 'yan sanda a shiyyar, Adisa Bolanta, ya ce tulun gas na na'urar sanyaya daki watau 'Air Condition' ne ya fashe abin da kuma ya janyo hadarin.

Za mu kawo muku karin bayani a nan gaba.