'Yan mata biyu sun tayar da bam a Kamaru

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kamaru ma na fama da hare-haren kungiyar Boko Haram kamar makwabciyarta Nigeria

Wasu 'yan mata biyu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne, sun tayar da wasu ababen fashewar da suke dauke da su a kofar shiga kasuwar sayar da dabbobi da ke garin Houmaka a lardin arewa mai nisa a Kamaru.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da safe.

Rahotanni na cewa 'yan matan biyu ne kawai suka mutu sakamakon fashewar abubuwan.

A baya-bayan nan dai an sha samun faruwar irin wannan lamari a Kamaru, inda 'yan mata ke tayar da bama-bamai.

Karin bayani