Amadou zai shiga zaben zagaye na biyu

Jagoran 'yan adawa a Nijar, Hama Amadou zai shiga takarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu na kasar da za a yi a ranar 20 ga watan Maris a cewar lauyansa,Mosi.

Lauyan Hama Amadoun, Mosi, ya kara da cewa gamayyar jam'iyyun adawar kasar ta COPA sun ce ba za su shiga tsare-tsaren yin zaben ba, amma Hama zai shiga zaben.

Kwanaki biyu da su ka gabata ne dai gamayyar jam'iyyun adawar kasar ta ce dan takararta Hama Amadou ba zai shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ba.

kakakin jam'iyyar Moden Lumana, Mahaman Laouali Leger ya fadawa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou cewa Hama Amadou ma na bayan matakin da COPA ta dauka na kauracewa Zaben.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tun a watan Nuwamban bara ne ake tsare da Hama Amadou a gidan-kaso, sakamakon zargin da ake masa na fataucin jarirai, amma ya musanta, yana cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne.

A zagayen farko na zaben dai, shugaba Muhammadou Issoufou ya samu sama da kashi 48 bisa dari na kuri'un da aka kada, inda ya rage kiris da ya samu adadin kuri'un da za su ba shi rinjaye a zaben.