MTN ya yi tayin biyan Naira biliyan 300

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tambarin kamfanin MTN

Kamfanin sadarwa na MTN ya yi tayin biyan tarar naira 300 biliyan wato dala biliyan daya da rabi ga gwamnatin Nigeria, wato kashi 40 cikin dari na tarar da kasar ta dora masa.

Tayin ya zo ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakin gwamntin Najeriya da kuma MTN.

Najeriya ta bukaci MTN ya biya tarar $5.2 biliyan saboda kin rufe layuka fiye da miliyan biyar da ba a yi wa rajista ba a shekarar 2015.

Sai dai daga bisani aka rage tarar da hukumar da ke sa idanu a kan kamfanonin sadarwa ta NCC ta dora wa MTN din zuwa $3.9 biliyan.

A farkon wannan makon ne shugaba Muhammadu buhari ya ce rashin rufe layukan da ba a yiwa rajistar ba ya taimaka wa 'yan kungiyar Boko haram, wadanda suka kashe daruruwan mutane a kasar.