'Mun fuskanci matsaloli a zagayen farkon na zabe'- CENI

Image caption Hukumar zaben Niger CENI ta ce za ta gyara matsalolin da aka fuskanta a zaben da ke tafe

A Jamhuriyar Nijar, hukumar zaben kasar CENI ta ce ta fuskanci matsaloli da dama a zaben shugaban kasa zagaye na farko gami da na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar 21 ga watan Fabrairun da ya gabata.

Matsalolin dai sun hada da rashin bude wasu rumfunan zabe a kan lokaci da karancin kayayyakin aikin zabe, da rashin sanin makamar aikin wasu jami'an zaben da wasu matsalolin da dama.

A wata hira da BBC, shugaban hukumar zaben CENI mai shari'a Bube Ibrahim ya ce za su gyara wadannan matsalolin ta yadda za a yi zaben shugaban kasar zagaye na biyu ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba.

A ranar 20 ga watan Maris ne dai za'a gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin Jagoran 'yan adawa a Nijar, Hama Amadou da shugaba Muhammadou Issoufou.