Niger: Hama Amadou na Asibiti

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Rahotanni sun ambato wani kakakin 'yan adawa na cewa an garzaya da Hama Amadou zuwa asibiti ne jiya Juma'a.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa an garzaya da Jagoran 'yan adawa a Nijar din, Hama Amadou zuwa asibiti a Yamai sakamakon matsalar wani ciwon ido da yake fama da shi.

Rahotanni sun ambato wani kakakin 'yan adawa na cewa an garzaya da Hama Amadou zuwa asibitin ranar Juma'a.

Tun a watan Nuwamban bara ne ake tsare da Hama Amadou a gidan-kaso, sakamakon zargin da ake yi masa na fataucin jarirai, amma ya musanta, yana cewa bi-ta-da-kullin siyasa ne.

A wannan makon ne kuma Lauyan Hama Amadoun, ya sanar da cewa gamayyar jam'iyyun adawar kasar ta COPA sun ce ba za su shiga tsare-tsaren yin zaben ba, amma shi Hamma zai shiga zaben zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.