Nigeria: wutar lantarki za ta inganta

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Gwamnatin Nigeria ta ce ta dukufa wajen ganin an inganta wutan lantarki.

Gwamnatin Najeriya ta roki al'ummar kasar afuwa bisa irin mawuyacin halin da suka shiga sakamakon matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a kasar a halin yanzu.

A wata sanarwa, Ministan watsa labarai na kasar Alhaji Lai Muhammed ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon karancin man Gas da kuma zagon kasa da wasu bata gari ke yi wajen satar na'urorin samar da wutar.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin ta dukufa wajen ganin an inganta wutan lantarki nan da karshen makon da ake ciki.

Rashin wutar lantarki a Najeriya na daga cikin manyan matsalolin da suka karya lagwan tattalin arzikinta, musamman ma ta bangaren masana'antu.