An fara ba 'yan gudun hijira tallafin kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za'a ba 'yan gudun hijira tallafin kudaden ne domin su sama damar magance wa su bukatun su.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hadin gwiwar Hukumar Samar da agajin gaggawa ta Nigeria wato NEMA sun soma wani shirin baiwa 'yan gudun hijira tallafin kudi.

Shirin dai ya soma ne da iyalai 'yan gudun hijira dubu 45 daga cikin 'yan gudun hijira sama da miliyan daya a jahar Borno.

A wata hira da BBC, Jami'in hukumar ta NEMA mai kula shiyyar arewa maso gabas, Alhaji Mohammed Kanar ya ce za'a ba 'yan gudun hijira tallafin kudaden ne domin su sama damar magance wasu bukatun su.

A watan da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai yi rangadin yankunan da aka kwato daga mayakan Boko Haram da zummar sanin ko yankunan sun cancanci a sake tsugunar da mazaunansu da suka kaurace wa hare-haren Boko Haram ko kuma a'a.