Sintiri a teku da jirgin sama mara matuki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayanan da jirgin sama mara matuki ya tattaro za'a rika aike wa da su ta tauraron dan Adam zuwa wani wurin bincike

Burtaniya za ta rika amfani da jirgin sama mara matuki don gano ma su kamun kifi ba bisa ka'ida ba a teku tare da kula da halittun ruwa.

Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta shata wani yanki a teku mai fadin murabba'in kilomita dubu 834,000 kusa da tsibirin Pitcairn a tekun Pacific a 2015.

Bayanan da jirgin mara matuki ya tattaro za'a rika aike wa da su ta tauraron dan Adam zuwa wani wurin bincike wanda zai taimaka wajen hukunta duk wa su da aka samu da kamun kifi ba bisa ka'ida ba.

An dai yi amannar cewa akwai kifaye da sauran halittun ruwa dabam dabam har fiye da 1,200 a tsibirin Pitcairns wadanda ba kasafai ake samun irin su a wasu tsibirai.