Bama-bamai sun tashi a Cameroun

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yankin Arewa mai nisa na Kamaru, ya saha fama da harin 'yan Boko Haram.

Rahotanni na cewa wasu bama-bamai sun fashe a Takolmari da ke yankin Arewa mai nisa a jamhuriyar Kamaru.

An ji karar fashewar abubuwan ne har sau biyu da safiyar yau.

Mahukunta dai ba su yi bayani akan ko samu asarar rayuka ko dukiya ba.

Yankin Arewa mai nisa na kasar, ya sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram, saboda makon da ya wuce wasu 'yan mata biyu 'yan kunar bakin wake sun ta da bama-bama a garin Houmaka, amma ba su samu nasarar hallaka kowa ba.