Brazil: Dilma na fuskantar matsin lamba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zangar tsige shugabar Dilma a Sao Paulo a shekarar 2015

Shugabar Brazil na fuskantar matsin lamba daga 'yan adawa a kan ta sauka daga mulki bisa zargin gaza bunkasa tattalin arzikin kasar. Zargin da ta musanta,

Masu zanga-zanga sun soma taruwa a manyan biranen Brazil domin gudanar da wata babbar zanga-zanga ta nuna kin jinin gwamnatin Dilma Rousseff.

'Yan adawa na son shugabar ta sauka saboda a cewarsu, ta kasa bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma hannu a wata gagagarumar badakalar cin hanci da rashawa.

Wadanda suka shirya zanga-zangar sun ce za a yi gangami a garuruwa 400 na kasar, ciki har da Sao Paulo a in da za a yi babbar zanga-zangar.