Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba za mu lamunci satar kudin gwamnati ba

Gwamnan jihar Niger da ke arewacin Najeriya, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce kawo yanzu gwamnatin sa ta kwato kusan Naira miliyan 500 daga jami'an tsohuwar gwamnati wadanda ake zargin sun sace daga kudin fansho.

Yayin wata ziyara a ofishinmu na London, Gwamnan ya ce gwamnatin sa na ci gaba da kokarin ganin ta kwato kudade daga hannun mutanen da ake zargi domin aiwatar da ayyuka ga al'ummar jihar.

A hirar su da Aliyu Abdullahi Tanko, Gwamnan Abubakar Bello ya ce tun da ya hau karagar mulki, ya gano cewar akwai kudaden gwamnati da suka yi layar zana.