Jirgin ruwan Koriya ta Arewa ya bata

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Koriya ta Arewa a yayin da ya zo kallon gwajin wani makami da jirgin kasarsa mai tafiya a karkashin ruwa ke harbawa.

Rahotanni na cewa koriya ta Arewa na neman wani jirginta mai tafiya a karkashin teku, bayan da ta daina jin duriyarsa a farkon makon nan.

Jirgin na aiki ne a kusa da bakin gabar kasar tsawon wasu kwanaki kafin ya bata.

Batar jirgin ya faru ne a lokacin da yanayin zaman dar-dar ya karu a yankin, da kuma daidai lokacin da Koriya ta Kudu da Amurka ke ci gaba da wani gagarumin atisayen sojoji.

Koriya ta Arewa ta sake yin wata barazanar yaki saboda atisayen, ta ce a shirye ta ke da ta kai hari da zaran ta ga alamun za a mamaye ta.