Trump ya hadu da zanga-zanga a Chicago

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi fito na fito tsakanin magoya bayan Trump da 'yan zanga, wanda hakan ya sa dantakarar ya soke hawa duro a Chicagon

Dan takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Donald Trump ya soke gangamin yakin neman zabensa na Chicago saboda zanga-zanga.

An samu yamutsi a cikin zauren taron da Mista Trump zai gudanar da yakin neman zabensa, ya yin da aka yi fito-na-fito tsakanin magoya bayansa da kuma daruruwan masu zanga-zanga wadanda suka yiwa wurin tsinke.

A wajen zauren taron kuwa, dubban masu zanga-zangan ne suka yi dafifi a inda wasu ke zargin dan takarar da nuna wariyar launin fata.

A martaninsa ga lamarin, Mista Trump ya ce, "wannan fushi na jama'a ba komai ba ne illa takaicin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki", sannan ya kara da cewa "an take masa 'yancinsa na fadin albarkacin bakinsa"