Yariman Saudiyya ya caccaki Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Obama a lokaci wata ziyara da ya kai Saudiyya

Wani Yarima a masarautar Saudiyya ya yi kakkausar suka ga shugaba Obama, bayan da Obaman ya nuna cewa Saudiyya na kasa a gwiwa wajen taimakawa Amurka magance matsalolin gabas ta tsakiya.

A wata budaddiyar wasika, Yarima Turki al-Faisal ya musanta cewa Saudiyya 'yar 'cin bulus ba ce'.

Yariman ya ce Saudiyya ta kasance a kan gaba wajen murkushe ayyukan kungiyoyin masu da'awar Musulunci ta hanyoyi daban-daban.

A cewarsa, Saudiyya ta yi musayar bayannan sirri wadanda suka taimaka wajen hana kai hare-haren ta'addanci a Amurka.